Type Here to Get Search Results !

Da dumi-dumi: : Ku mayar da N1000 da N500 ofishin CBN, zamu fito da tsaffin N200 a cigaba da amfani, Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari ya kara wa’adin mayar da tsaffin takardun Naira bankuna da kwanaki 60.  Legit.ng ya wallafa
.

Shugaban kasan ya sanar da hakan yayin jawabin da ya gabatar a safiyar nan daga fadar shugaban kasa. 

Buhari ga bayyana cewa ya umurci Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya fitar da tsaffin kudade na N200 saboda mutane su cigaba ca amfani da kudadensu tsawon kwanaki 60. 

Amma bai amince a cigaba amfani da tsaffin 500 da 1000 ba, kawai bankunan CBN za’a iya mayarwa. 

Na umurci CBN yayi amfani da dukiyar gwamnati da ya hallata a doka don wayar da kan yan kasa, su samu sabbin kudi cikin sauki kuma mutane su iya kai kudinsu banki." 

Hakazalika na umurci CBN ta hada kai da hukumomin yaki da rashawa don tabbatar da cewa babu wanda yake kokarin yiwa wannan aiki da suke yi zagon kasa." 

Don saukakewa al'ummarmu lamari, na bada izini ga CBN a fito da tsaffin takardun N200 saboda mutane su cigaba da amfani da su tare da sabbin N200, N500, da 500 tsawon kwanaki 60 zuwa ranar 10 ga Afrilu, 2023 da za'a daina amfani da su." 

Dukkan tsaffin N1000 da N500 kuma a mayar da su bankin CBN kadai"

BY ISYAKU.COM

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies