Rikicin zabe ya barke a Ribas, Yan bindiga sun harbi mata biyu masu zabe a Bayelsa


Mata biyu sun jikkata sakamakon harbin bindiga yayin da rikici ya barke ana tsaka da gudanar da zabe a gudunmar Ofoni da ke mahaifar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo. 

Wani ganau wanda ya je kada kuri'a a rumfar zaben, ya bayyanawa jaridar Daily Trust a ranar Lahadi cewa wasu fusatattun matasa uku daga garin sun harbi wata matashiya kan wani sabani da ya gibta a tsakaninsu. Legit.ng ya wallafa.

Kamar yadda ya bayyana, faruwan al'amarin ya kawo tsaiko a tsarin gudanar da zabe a yankin.

A cewarsa, harbin ya sake samun wata mata mai matsakaicin shekaru inda aka gaggauta daukarta zuwa wani asibiti da ke kusa.

An tattaro cewa dandazon jama'ar da ke wajen sun kama biyu daga cikin yan daban da suka kawo hatsaniyar sannan suka mika su ga jami'an tsaro.

A Ribas, an tattaro cewa rikici ya barke a wasu kananan hukumomin jihar. An tattaro cewa jam'iyyar siyasa mai jagoranci a jihar ta ci zarafin wasu masu zabe kan wani dan takara da suke so a zaba.

Jaridar Punch ta kuma rahoto cewa wata tawagar yan sanda ta kama wakilinta, Gbenga Oloniniran a kusa da gidan Gwamna Nyesom Wike in Rumuiprikon, karamar hukumar Obio/Akpor ta jihar.

Oloniniran, wwanda ya je aikin zabe yana ta daukar hotunan inda jami'an yan sanda ke kama wasu matasa a wata rumfar zabe lokacin da jami'an tsaron suka damke shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN