Type Here to Get Search Results !

Mata mai juna biyu ta yanke jiki ta fadi ta mutu a layin kada kuri'a a Zamfara


A rumfar zabe da ke yankin Tsafe a jihar Zamfara ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, wata mata mai juna biyu mai suna Shamsiya Ibrahim ta yanke jiki ta fadi ta mutu a lokacin da take jira a layi domin kada kuri’arta. Intelregion ta ruwaito.

Marigayiya Shamsiya ta yi tattaki ne daga yankin Kotorkoshi da ke karamar hukumar Bungudu zuwa garin Tsafe mai tazarar kilomita 50 domin kada kuri’arta.  

An garzaya da ita babban asibitin Tsafe inda aka tabbatar da rasuwar ta bayan isar ta.

Har yanzu hukumomi ba su bayar da wata sanarwa a hukumance ba game da wannan mummunan lamari.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies