Daruruwan shaguna sun kone sakamakon tashin gobara akasuwar Monday Market da ke Maiduguri a jihar Borno vewar rahotanni.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gobarar ta fara da misalin karfe 2:00 na tsakar daren ranar Lahadi, 26 ga watan Fabrairu kuma ta yadu zuwa bangarori daban-daban na kasuwar.
A daidai lokacin kawo wannan rahoton, ba a san musababbin abun da ya haddasa gobarar ba kuma jami'an kwana-kwana na nan suna kokarin kashe wutan. Legit ya wallafa.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa gobarar ta lakume daruruwan shaguna yayin da aka yi asarar dukiya na miliyoyin naira.
BY ISYAKU.COM