Mahaifin yar makaranta mai shekara 7 ya mutu lokacin fuskantar Yakubu direban motar makaranta da ya yi lalata da diyarsa

 


Wani magidanci dan birnin Legas mai shekaru 47, Frederick  ya rasa rans sakamakon arangama da wani direban bas a makaranta wanda ake zargi da lalata ‘yarsa ‘yar shekara bakwai.


 Ya rasu ne a harabar makarantar a wani artabu da direban da aka fi sani da Yakubu.


 Frederick ya je ya sadu da shugabannin makarantar tare da gwauruwar sa da ’yarsu don ya ba da labarin abin da ‘yarsu ta fuskanta game da Yakubu kuma ya nemi a É—auki mataki nan take.


 Bayan ya mutu a rikicin, Yakubu ya tsere daga wurin da lamarin ya faru, lamarin da ya sa ‘yan sanda suka fara farautarsa.


 Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce ‘yan sanda suna bin direban motar kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai an gurfanar da shi a gaban kotu.


 Matar Frederick ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN cewa ‘yarta ta ba ta labarin yadda Yakubu ke kai ta gidansa da ke Ajuwon a Ogun don lalata da ita.


 Ta ce ta ba wa mijinta da ya rasu irin wannan rahoto, daga nan ne ya kira makarantar aka ce ya zo domin a sasanta.


 “A ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu, ‘yata ta gaya min cewa direban motar makarantarta ya kai ta gidansa da ke Ajuwon, a kan cewa yana bukatar ya ajiye wani abu a gida kuma ta bi shi.


 “Lokacin da suka shiga gidan, direban yakan ce wa ‘yata ta zauna a kan cinyarsa;  ta daga uniform dinta na makaranta ta sumbace shi a baki. “Na gaya wa mijina abin da ‘yarmu ta ce a ranar Litinin, 6 ga watan Fabrairu, nan take ya kira makarantar ya kai kara ya ce shi ma zai kai rahoton zargin ga ‘yan sanda.


 “An ce masa ya fara zuwa makarantar don haka muka je ranar Talata 7 ga watan Fabrairu muka hadu da mai makarantar da direba da wasu malamai.


 “Mai makarantar bayan ya saurare mu;  ya fuskanci direban, ya ce ya dawo a makare da motar makaranta a makon da ya gabata, da aka tambaye shi, sai ya ce ya je ya sauke wani abu a gida.


 “Daga baya an tambaye shi game da zargin da ake yi masa, amma ya musanta.  Sai aka tambayi 'yata ta ba da labarin irin abin da ta gaya mana a gida.


 "Direban bai iya cewa komai ba in ban da tambaya: 'ni'?  'ni'?, 'ni'?


 “Mijina wanda a bayyane ya fusata ya je wurin direban ya daka masa tsawa ya tambaye shi dalilin da ya sa ya lalata da ‘yarsa.


 “Mijina a fusace ya mari direban sai suka fara fada inda ya ture mijina a kirjinsa.  Ya fadi kuma kokarin farfado da shi ya ci tura.


 “Mun garzaya da shi asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa,” inji matar.


 Ta kara da cewa Yakubu ya arce bayan faruwar lamarin inda daga bisani ta kai kara ofishin ‘yan sanda na Iju.


 Daraktan makarantar, ya ki yin magana a kan lamarin yana mai cewa yana taimaka wa ‘yan sanda wajen farautar Yakubu, direban bas din makarantar da ya arce. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN