Rahotanni daga garin Argungun a karamar hukumar Argungu jihar Kebbi na cewa ana zargin wani saurayi ya rataye kanshi har Lahira.
Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi 12/2/2023 da awannin tsakiyar rana.
An gano gawar yaron, (Mun sakaya sunansa) ana zargin dan kasa da shekara 20, ya rataye kanshi ne a wani bandaki da ke bayan dakin mahaifiyarsa a Unguwar Tudun wada a Birnin Argungu.
Bayanai na cewa za a yi jana'izarsa da karfe biyar na yammacin ranar Lahadi a garin Argungu.
Babu wani bayani kan musabbabin faruwar wannan lamari kawo yanzu.
Kakakin hukumar Yan sandan jihar Kebbi SP Nafiu Abubakar ya tabbatar da faruwar larin, ya ce " Mun sami rahotun faruwar lamarin" inji SP Nafiu.
Karin bayani na nan tafe...
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI