Matsalar canjin sabbin kudi: Wani Gwamnan APC na 5 a Arewa ya maka Buhari da CBN a Kotu


 Gwamnatin jihar Neja ta shigar da karar gwamnatin tarayya a dalilin tsarin da bankin CBN ya fito da shi na canza wasu takardun kudi. Legit.ng Hausa ya wallafa.

The Cable da ta fitar da rahoton ta bayyana cewa Neja ta zama jiha ta biyar da za tayi shari’a da gwamnatin Muhammadu Buhari a kan tsarin kudin.

Kafin yanzu, gwamnatocin Kaduna, Kogi, Zamfara da kuma Kano duk sun yi karar gwamnatin tarayya, su na so a koma amfani da tsofaffin kudi.

Kwamishinan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin jihar Neja, Nasara Danmallam ya fitar da jawabi cewa sun kai kara gaban koli.

Kara ta je kotun Allah ya isa

Danmallam ya fitar da jawabi, yana cewa kararsu mai lamba SC/CV/210/2023 tana kotun koli tun a ranar Juma’a, su na sa ran a biya masu bukata.

Mai girma Kwamishinan ya ce su na rokon babban kotun kasar ta tsawaita wa’adin da bankin CBN ya bada na canza N200, N500 da kuma N1000.

Lauyoyin Gwamnatin Neja sun sanar da Alkalan kotun cewa karancin sababbin takardun kudin ya jefa al’ummar jihar Neja cikin mawuyacin hali.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, mutanen karkara sun fi shan wahalar tsarin sauya kudin, don haka Kwamishinan ya ce suke neman ceton mutane.

A matsayinsa na Kwamishinan shari’a, Nasara Danmallam ya nuna gwamnatinsu za tayi duk abin da za ta iya domin ganin an raba jama’a da wahala.

Kwamishinan yake cewa za su bi duk wata hanya da ba ta sabawa dokar kasa ba. Legit.ng Hausa ba ta da labarin ko an sa lokacin sauraron shari’ar.

Gwamnatin tarayya ta kalubalanci hukuncin farko da aka yi, za a koma kotu a ranar Laraba.

2 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. Yayi dai dai malam haka ya kamata wallahi mutane suna wahala a kan abin da bai zama wajibi ba

    ReplyDelete
  2. Allah duk Wadanda ke son wahalda talakawa Allah ka wahar she su ko bayan sun bar mulki

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN