Daga daga cikin hadiman ofishin uwar gidan shugaban kasa, Zainab Kassim ta shigar da kara kan take hakkin da Aisha Buhari ta yi, inda ta nemi a bata diyyar N100m.
Legit Hausa ta wallafa cewa sauran wadanda ke cikin karar sun hada da sufeto janar na 'yan sandan Najeriya da hukumar tsaro ta farin kaya; DSS.
Zainab ta yi ikrarin cewa, Aisha Buhari ta umarci jami'an DSS da su kwamushe ta tare da kai ta Villa inda uwar gidan sugaban kasan ta ci zarafinta da kuma kokarin lahantata tare da taimakon jami'an DSS da 'yan sanda saboda ta goge wani rubuta a kafar sada zumunta.
Karar mai lamba FHC/ABJ/05/2021 da wakilin Punch ya samo a ranar Juma'a 17 ga watan Faburairu ta nemi kotu da ta ayyana kama da tsare a matsayin haramtaccen aiki kuma abin ki.
Aisha Buhari ta sa an dauko mata wata mata, an kai ta kara kotu
Lokacin da abin ya faru da kuma abin da ya faru
Wani yankin karar ya bayyana cewa, an kama tare da tsare hadimar ne a tsakanin ranakun 18 zuwa 22 ga watan Nuwamba.
Ta kuma roki kotun da ta tabbatar da hana 'yan sanda da jami'an DSS sake kama ta, tsare ta da cin zarafinta a nan gaba saboda ba ta laifi.
Hakazalika, ta roki kotu da ta umarci jami'an tsaron da su ba ta wayarta kirar Samsung Note 20 Ultra tare da umartar Aisha Buhari da hukumomin tsaron biyu su ba ta diyyar N100,000,000.
Ya zuwa yanzu dai ba a ba karar alkalin da zai shari'a ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Hakazalika, majiya ta yi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun uwar gidan shugaban kasa, Mr. Aliyu Abdullahi amma ba a yi nasarar samunsa ba.
An samu dambarwa tsakanin Aisha Buhari da wani matashin dalibi dan jihar Bauchi, inda aka kama shi aka kaishi Villa kafin daga bisani aka zarce kotu dashi a zargin ya zagi uwar gidan shugaban kasa.
BY ISYAKU.COM