Karya ne: Buhari ya gaji, ya karyata zargin El-Rufai da Ganduje na hana ayi zabe

 

A ranar Juma’a, 17 ga watan Fubrairu 2023, Gwamnatin tarayya ya karyata zargin da ake yi cewa ana kokarin a kafa gwamnatin rikon kwarya. Legit ta wallafa.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin TVC, Ministan yada labarai da al’adu na kasa watau Alhaji Lai Mohammed ya ce sam labarin ba gaskiya ba ne.

Ministan tarayyan yake cewa wasu ne suka kitsa labarin karyar saboda su hargitsa kasar nan.

Lai ya kara da cewa Bola Tinubu ne zai lashe zaben shugaban kasa, ma’ana jam’iyyar APC za ta cigaba da mulki ba tare da an daura gwamnatin riko ba.

“Abin da yake zahiri shi ne Shugaba Muhammadu Buhari har ya kafa kwamitin mika mulki, kuma da yardar Ubangiji, ‘dan takaran APC ne zai gaje shi duk karyayyakin da ake fada.
‘Dan takaran jam’iyyar APC ya shiga ko ina yana kamfe fiye da sauran ‘yan takaran. Shugaban kasa, jam’iyya da kuma gwamnati duk su na goyon bayan shi (Bola Tinubu)."

- Lai Mohammed

Vanguard ta rahoto Ministan yana cewa shekaru 20 da suka wuce Tinubu ya fara harin mulki, yana goyon bayan ‘yan takara daga sauran yankunan Najeriya.

"Ribar menene Buhari da jam’iyya za ta samu idan ba a goyi bayan Tinubu ya zama shugaban kasa ba?
Hallaka ne wani a gwamnatin nan ya ki goyon bayan Tinubu domin idan wata jam’iyya ta karbi mulki, abin ba zai yi kyau ba."
- Lai Mohammed

Martanin Garba Shehu

A wani jawabi dabam a Twitter, an ji Malam Garba Shehu yana mai karyata batun, ya ce Muhammadu Buhari ba ya shirye-shiryen kawo gwamnatin riko.

Hadimin shugaban kasar yake cewa an saba kin sallama gwamnati a Afrika, amma Buhari bai da wannan nufi, kuma yana goyon bayan takarar Bola Tinubu.

Shehu ya ce adawar 'dan takaran na APC ga sauyin kudi a irin wannan yanayi, bai nufin ba ya goyon bayan tsarin takaita yawon kudi da aka fito da shi.

Zargin da Abdullahi Ganduje yake yi
A wani rahoto, an ji labari Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya zargi Shugaban Kasa da ‘kashe’ Jam’iyyar APC a lokacin da zai bar kan karagar mulki.

Abdullahi Ganduje ya ce ana kokarin kafa gwamnatin rikon kwarya irinta Cif Ernest Shonekan.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN