Rikici ya barke a sassa daban-daban na Legas a safiyar ranar Juma’a, 17 ga watan Fabrairu, yayin da ake zargin matasa sun yi barna kan rashin samun kudi.
Bidiyon da suka fito daga yankunan Mile 12, Agege, Ketu, Ojota, da dai sauransu a jihar Legas, sun nuna yadda jama’a suka toshe hanyoyi tare da far wa matafiya dake kan hanyarsu ta zuwa aiki.
A wani faifan bidiyo, an ji wani mutum yana cewa sai da ya koma baya saboda harbin da aka yi masa a Mile 12. Daga nan sai ya shawarci wadanda ke Ikorodu su ci gaba da zama a can, kada su kuskura su shiga Mile 12.
Masu amfani da shafin Twitter da ke zaune a yankunan da ake fama da rikici sun yi ta yada hotunan bidiyo da ke nuna tashe tashen hankula a yankunansu.
Da yake mayar da martani, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Gaskiya ne. Mutanenmu suna can. An tura sassan Æ™arfafawa. A zauna lafiya a can yayin da muke sa ido sosai da sarrafa lamarin.
A cikin wani sakon twitter da ya biyo baya, Hundeyin ya rubuta: “An dawo da zirga-zirgar ababen hawa da mutane gaba daya. Jami’an mu har yanzu suna nan a wanen don hana tabarbarewar doka da oda.
BY ISYAKU.COM