Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano a ranar Alhamis ta raba auren Asiya Ganduje, diyar Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, mai shekara 16. Jaridar vanguard ta ruwaito.
Asiya ta garzaya kotu tana neman a raba aurenta da mijinta, Inuwa Uba, saboda ta gaji ta koshi da zaman aure wanda ya haifar da ‘ya’ya hudu.
Alkalin kotun, Khadi Halliru Aliyu ya raba auren ne a lokacin da yake yanke hukunci kan lamarin a ranar Alhamis.
Sai dai Khadi Aliyu ya umarci diyar Ganduje da ta mayar wa mijinta Uba, sadakin N50,000 a matsayin asarar da ya yi.
Kotun ta kuma yi watsi da bukatar mijin Asiya na neman takardun kadarorin da ya ce nasa ne.
Lauyan wanda ya shigar da kara ( diyar Ganduje), Ibrahim Nassarawa, ya ce kotun ta yanke hukuncin ne bisa abin da ya kamata ya zama tushen auren wanda shi ne sadaki.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, Lauyan maigidan Umar I. Umar ya ce za su yi nazari kan hukuncin kuma za su jira mataki na gaba daga wanda yake karewa kan ko za su kai ga kotun daukaka kara a kan lamarin ko a’a.
Ya ce sun yi iya kokarinsu wajen daidaita dangantakar da ke tsakaninsu musamman yadda ta haifa masa ‘ya’ya hudu amma ba ta samu sakamakon da ake so ba.