Wata kotun shari’a da ke zamanta a yankin Filin Hoki a jihar Kano ta tasa keyar wata shahararriyar ‘yar TikToker mai suna Murja Kunya zuwa gidan yari bisa zarginta da aikata laifuka da suka saba wa koyarwar addinin Musulunci da kuma yin barazana ga mutane a dandalin. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
An gurfanar da TikToker a gaban mai shari’a Abdullahi Halliru bisa tuhume-tuhume biyu da suka hada da yin barazanar kai hari ga wasu mutane da kuma fitar da bidiyoyin zuga wadanda suka saba wa ka’ida da koyarwar Musulunci, wadanda kuma za su iya haifar da kuskure.
Kunya ta musanta zargin da ake mata. Yayin da lauyanta, Barista Yasir Musa, ya bukaci kotun da ta tura ta hannun Hisbah ko kuma ‘yan sanda a maimakon gidan gyaran hali, sai lauyan da ke adawa da shi, Barista Lamido ABBA Soron Dinki ya ki amincewa da hakan a gaban Kotu.
Mai shari’a Halliru wanda ya dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga Fabrairu, 2023, domin ci gaba da sauraron karar, ya bayar da umarnin a tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali.
To Allah yasa wannan hukunchin yazama shine silar shiriyarta amin
ReplyDelete