Type Here to Get Search Results !

Karancin Naira: 'Yan Najeriya sun gaji da jira, sun fara zanga-zanga a bankuna


Wasu gungun mutane a jihar Legas sun shirya wata zanga-zanga a hedkwatan bankunan kasuwanci da yawa a birnin Legas. Legit.ng ya ruwaito.

A wani bidiyon da aka yada a kafar sada zumunta, ‘yan zanga-zangan sun zargi bankuna da kin bin ka’idar CBN game da sabbin kudi, lamarin da ya ke ba talakawan kasar wahala.

An shirya wannan zanga-zanga ne karkashin kungiyar farar hula ta Coalition of Civil Society Organizations for Good Governance, (CCSGG).

A lokacin zanga-zangar, kungiyar ta yi kira ga bankuna da su saki sabbin Naira ga kowa a Najeriya don ci gaba da harka yadda aka saba.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies