An Kuma: Adam A Zango na shirin rabuwa da matarsa ta shida


Fitaccen jarumi a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Adam A. Zango na dab da rabuwa da matarsa, Safiya Chalawa. Jaridar Aminiya ta ruwaito.


A wani faifan bidiyo da ya fitar, jarumin ya bayyana cewa matar tasa ta zabi kasuwancinta a kansa, wanda hakan ya sa babu yadda zai yi face ya hakura da ita.


A karshe ya ce za a ji labarin daga baya, amma kada a yi masa mummunar fassara.


A cewarsa, ba zai kara aure idan har ya rabu da matarsa Safiya, inda ya kara da cewa dama yana yawan aure ne bayan rabuwa da wata domin ya gujewa fadawa zinace-zinace, musamman saboda daukakar da Allah Ya yi mi shi.


Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a, 25 ga watan Afrilun shekarar 2019 ce aka daura auren jarumin da amaryarsa Safiya a Fadar Sarkin Gwandu a Jihar Kebbi.


Safiya ce matar Zango ta shida


Kafin ita, ya auri Amina, wadda ita ce maman Haidar a shekarar 2006. Sai Aisha ce ta biyu, wadda ya aura a garin Shika da ke Kaduna. Ita ta haifa masa yara uku.


Matarsa ta uku sunanta Maryam, wadda ya aura a Jihar Nasarawa, sannan ya aura ta hudu ita ma mai suna Maryam AB Yola, wadda ta fito a fim din Nas, wadda ya aura a matsayin a garin Yola na Jihar Adamawa.


Sai a shekarar 2015 jarumin ya aura Ummukulmsum a garin Ngaoundere na kasar Kamaru, ita ma haifa masa yarinya, Murjanatu.


Sai kuma matarsa Safiya, wadda ita ce ta shida.


Bayan aurensu, an sha yi wa Safiya shagube cewa Zango zai rabu da ita, inda take nuna cewa mutu ka raba.


Safiya, wadda take kasuwanci a kafofin sadarwa, tana yawan nuna soyayyarsu da jarumin ta hanyar sanya hotunansu ko dai a tare, ko sanya hotonsa ta yi rubutun soyayya.


Sai dai Aminiya ta leka shafinta na Instagram, inda ta ga karshen hotonsa da Safiya ta saka shi ne a ranar 30 ga Satumban bara na bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN