Majalisar Kansilolin Karamar Hukumar Sumaila a Jihar Kano ta tsige Shugaban Karamar Hukumar, Honorabul Ibrahim Hamisu Rimi kan zargin sa da almundahana. Jaridar Aminiya ta ruwaito.
Yayin zaman majailsar a ranar Laraba, Kansila mai wakiltar mazabar Gani, Isma’il Sabi’u Salisu, ne ya fara gabatar wa majalisar kudirin tsige shugaban karamar hukumar bisa wadansu zarge-zarge.
Zarge-zargen sun hada da na karkatar da wasu kudaden karamar hukuma da kuma yi wa dokokin Najeriya karan tsaye wajen aiwatar da ayyuka ba tare da sahalewar majalisar kansilolin ba.
Bayan gabatar da kudirin ne duk kansilolin suka amince da tsige shugabar karamar hukumar, kamar yadda Shugaban Majalisarsu, Honorabul Mustapha Garba Haladu ya shaida wa manema labarai.
A nasa bangaren Honorabil Nuhu Ado Gala, shugaban masu rinjaye na majalisar kansilolin Karamar Hukumar Sumaila ya tabbatar wa Aminiya da matsayarsu ta maye gurbin shugaban karamar hukumar da mataimakinsa Honorabil Abubakar Musa Kuliya nan take.
Majalisar ta bukaci sabon shugaban karamar hukumar da ya gaggauta daukar mataimakinsa domin ci gaba da ayyukan da za su ciyar da karamar hukumar ta Sumaila gaba.