Duba hukuncin da ke jiran El-Rufai da Ganduje kan maganar Canjin kudi, Minista ya magantu


Ministan sharia kuma babban lauyan Gwamnatin Najeriya Abubakar Malami ya magantu a kan wadanda suka rika maganganu kan canjin kudi. Legit.ng ya wallafa.

A dalilin tsarin canza takardun Naira da aka yi, wasu mutane har da Gwamnoni sun yi ta maganganu, Daily Trust ta rahoto cewa ana shirin bincike.

Abubakar Malami SAN ya shaida cewa jami’an tsaro za su dauki mataki bayan sun kammala binciken wadannan mutane da zargin cin amanar kasa.

Ministan shari’a na kasa ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyi daga wajen ‘yan jarida a fadar shugaban kasa na Aso Villa a ranar Alhamis.

Gwamnoni sun ja daga da gwamnati
Rahoton ya ce a cikin Gwamnonin jihohi, Mai Girma Nasir El-Rufai da Abdullahi Umar Ganduje sun fi kowa sukar tsarin nan da bankin CBN ya fito da shi.

Abin ya kai sai da wasu Gwamnoni suka shigar da karar gwamnatin tarayya a kotun koli.

AGF: 'Akwai zargin cin amanar kasa'
Da ake zantawa da shi, Malami SAN bai ambaci sunan kowane Gwamna ba, amma ya ce kalamansu za su iya zama cin amanar kasa, kuma za a bincike su.

Mai girma Ministan yake cewa jami’an tsaro za su yi wannan bincike, sannan a yanke hukunci idan har akwai wani mataki na gaba da ya dace a dauka.

A jawabinsa, Ministan ya sake jaddada matsayar gwamnati na cewa wasu daidaikun mutane ne suka saci kudi, ana kokarin amfani da shi wajen murde zabe.

A matsayinsa na AGF, Malami ya ce canza kudin zai ba al’umma damar ganin wanda suke kauna ya lashe zabe, a maimakon attajirai suyi amfani da dukiya.

Ministan ya ce makasudin tsarin shi ne a tsabtace zabe domin gwamnati ta na kokarin kawo gyara. Jaridar nan ta This Day ta fitar da wannan labari.

Akwai yiwuwar binciken masu sakin kalamai, Ministan kasar ya ce wannan aikin jami’an tsaro ne, daga nan sai a dauki matakin laifin da ya kira bore.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN