DIG, AIG na Yan sanda sun dira jihar Kebbi don zaben 2023, an gudanar da zagayen baje karfin tsaro a Birnin kebbi


Mukaddashin shugaban Yan sandan Najeriya ya dira jihar Kebbi ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu domin gudanar da harkar tsaro lokacin zaben 2023. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

DIG Hafiz Muhammad Nura, daga Shelkwatar Yan sandan Najeriya ya shaida wa manema labari cewa ya zo jihar Kebbi ne domin jagorantar harkar tsaro a lokacin zabe a jihar.

Kafin isowarsa, mataimakin Safeto janar na yan sanda shiya na 14 AIG Edwar Egbuka, ya dira jihar Kebbi kan lamarin tafiyar da tsaro a fadin jihar lokacin zabe.

Tun farko dai, an gudanar da zagayen baje kolin karfin tsaro na gamayyar jami'an tsaron jihar Kebbi karkashin jagorancin Kwamishinan Yan sandan jihar Kebbi CP Ahmed Magaji Kontagora.

Motoci dauke da gamayyar jami'an tsaro sun zagaya cikin garin Birnin kebbi da suka hada da Tudun wada, Gangaren 'Yar Yara, Tsohon gari, Makerar gandu, Badariya, Gesse da sauransu.

Zagayen ya hada da jami'an rundunar Yan sanda, Nigeria Army, DSS, Immigration Service, Custom Service, Civil Defence NSCDC da Nigeria Correctional Service.

Latsa kasa ka kalli bidiyo.

Baje kolin karfin tsaro, Latsa kasa ka kalli bidiyo


Sintirin maraba da AIG, latsa kasa la kalli bidiyo


Latsa nan ka kalli Hotuna


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN