Da dumi-dumi: 'Yan sanda sun haramta duk wani gangami a Kano yayin da magoya bayan manyan jam'iyyun siyasa 2 suka yi arangama


Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta soke duk wani nau’in gangamin siyasa saboda rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP). Legit.ng ya wallafa.

 Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rikicin ya barke ne yayinda bangarorin biyu karkashin jagorancin gwamnan jihar Abdullahi Ganduje na jam’iyyar APC da kuma Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar NNPP suka shirya gangamin yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a wannan rana, Alhamis 23 ga watan Fabrairu.  .

 Rikicin ya samo asali ne bayan da hukumomin ‘yan sanda suka gayyaci shugabannin jam’iyyun APC, PDP da NNPP domin gudanar da wani taron gaggawa, inda suka gargadi jam’iyyun kan tashin hankalin da aka samu a yayin taron.

 An tattaro cewa APC da NNPP sun yi watsi da shawarar da hukumomin tsaro suka ba su, inda suka ci gaba da gudanar da gangamin da aka shirya gudanarwa, wanda ya haifar da kazamin fada tsakanin jam’iyyun.

 Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu ’yan daba ne da ba a san ko su waye ba suka kai wa magoya bayan jam’iyyar NNPP hari inda suka kona motocinsu a kan hanyar Zariya.

 Majiyoyi sun ce za su je Kwanar Dangora ne domin tarbar Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, wanda ke hada gangamin yakin neman zaben sa a lokacin da lamarin ya faru.

 A halin da ake ciki, wasu jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki sun ce sun yi niyyar fara taron su ne a titin Club.  Sabanin haka, NNPP ta ce suna so su fara nasu ne a Kwanar Dangora kafin su wuce gidan Kwankwaso da ke Miller Road, off Club road.

 Sai dai kuma, ‘yan daba dauke da muggan makamai daban-daban suna ta yawo cikin walwala a cikin birnin tun ranar Litinin, abin ya rutsa da wasu da dama, in ji wata majiya.

 ‘Yan sanda sun tabbatar da soke taron siyasa a Kano

 Da yake tabbatar da soke duk wani gangamin siyasa a jihar, DCP Muhammed ya ce:

 “Kun tuna cewa jam’iyyun siyasa uku (3) ta APC, NNPP, da PDP sun sanar da umarnin taron nasu da aka shirya gudanarwa ranar Alhamis, 23 ga Fabrairu, 2023, a cikin babban birnin Kano.

 “Bisa la’akari da yanayin tsaro da ake fama da shi a jihar da ma kasa baki daya, kwamishinan ‘yan sandan ya kira wakilan jam’iyyun siyasa uku zuwa wani taron gaggawa domin lalubo bakin zaren warware matsalar.

 "Saboda haka shawara ce dukkan jam'iyyun siyasa su dage taron da aka shirya na shugaban kasa/majalisar tarayya zuwa wani lokaci bayan zaben ranar 25 ga Fabrairu."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN