Dan takarar gwamnan jihar Cross River na jam’iyyar Peoples Redemption Party, Usani Usani, a ranar Alhamis, ya tsallake rijiya da baya a wani hari da maciji ya kai masa a gidan sa dake unguwar Mkpani a karamar hukumar Yakurr.
Ku tuna cewa Usani, wanda tsohon ministan harkokin Neja Delta ne, ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi da aka yi a kan babbar hanyar tarayya ta Calabar zuwa Ikom a kan hanyarsa ta zuwa garinsu.
An harbe mutane biyu tare da sace wasu uku a harin wanda ya faru a makon jiya.
Kakakin dan takarar gwamnan, David Agabi, wanda ya tabbatar wa jaridar Punch lamarin na baya-bayan nan, ya ce an kai wa maigidan nasa hari ne a lokacin da ya ke yawo a gidansa da tsakar rana.
"Dan takarar gwamna yana unguwar sa Mkpani a karamar hukumar Yakurr yana fita daga gidansa. Ya kusa taka macijin amma ya rasa. Mutane sun zo sun kashe shi" Yace.
?Wannan ya yi yawa. Jama'a na shirin kashe Usani, bayan wani yunkurin kashe shi da bai yi nasara ba; yanzu sun aiko maciji,? Ya kara da cewa.
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI