Shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya shiga ganawar sirri da daukacin gwamnonin jam'iyyar yanzu haka.
Legit ta ruwaito Gwamnonin dake hallare sun hada da Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, Gwamna Simon Lalong na Plateau, da gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja.
Hakazalika akwai Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe da kuma Gwamna Muhammad Inuwa na jihar Gombe.
Karin bayani na nan tafe...
BY ISYAKU.COM