Tap di: Ganduje, El-Rufai da wasu Gwamnoni da suka ki bin umurnin Buhari, suka halasta amfani da tsaffin kudi a Jihohinsu

Duk da umurnin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bada a jawabinsa na ranar

Alhamis, 16 ga watan Fabrairun 2023, na fada wa yan Najeriya cewa tsohon N200 ne kadai ya halast a kashe har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun 2023, wasu gwamnonin jihohi sun fada wa mutanensu su cigaba da amfani da tsaffin N500 da N1000. Legit.ng ya wallafa.

Gwamnonin sun ce halas ne a cigaba da kashe tsaffin N500 da N1000 har sai kotun koli ta yanke hukunci kan lamarin a ranar 22 ga watan Fabrairun 2023.

Gwamnoni sun yi watsi da umurnin shugaban kasa
A cewar gwamonin, hukuncin kotun koli ne kadai abin yi wa biyayya.

Idan za a iya tunawa kotun kolin ta umurci CBN ta bari a cigaba da kashe tsaffin nairan tare da sabbi bayan karewar wa'adin ranar 10 ga watan Fabrairu.

A ranar Talata, 14 ga watan Fabrairun 2023, CBN sanar cewa haramun ne amfani da amfani da tsaffin kudi ta bukaci yan Najeriya su mayar da kudaden zuwa rassan ta.

Babban bankin ta kuma bude shafin intanet don yan Najeriya su mayar da tsaffin kudinsu.

Wannan sanarwar ta CBN ta tada hankulan mutane a sassar kasa inda mutane ke ta rububin zuwa banki su kai kudinsu.

Amma gwamnonin jihohi da dama sun dage cewa za su bi umurnin kotun koli kuma sun fada wa mutanen jihohinsu su cigaba da amfani da tsaffin kudin da CBN ta ce an dena amfani da su.

Har yanzu hukuncin kotun koli yana nan daram-dam, Antoni Janar na Legas
Bayan jawabin Buhari, Antoni Janar na Legas kuma kwamishinan shari'a Moyosore Onigbanjo ya ce har yanzu hukuncin kotun kolin kan sauya fasalin nairan yana nan daram-dam.

Onibanjo ya ce gidajen mai, bankuna, da sauran hukumomi da ke saba umurnin kotun kolin za su iya fuskantar hukunci.

The Punch ta rahoto cewa Onibanjo ya bayyana hakan ne a shirin Business Show na TVC a ranar Alhamis 16 ga watan Fabrairu bayan jawabin Buhari.

Gwamnan Kaduna ya bijire wa umurnin Buhari na haramta amfani da tsaffin N500 da N1000

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai shima ya ayyana cewa halas ne a cigaba da kashe tsaffin kudin a jiharsa har sai lokacin da kotun koli ta ce ba haka ba.

A cewar rahotanni, El-Rufai ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi wa jihar a ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairu bayan jawabin Buhari.

Kano ta dage kan hallarcin tsaffin nairorin
Duk da jawabin da Buhari ya yi na dena amfani da tsaffin N500 da N1000, gwamnatin jihar Kano ta ce za ta hukunta duk wani banki, da kamfani ko kasuwanci da masu POS da ke kin karbar tsaffin naira.

Gwamnan na Kano ya bada umurnin kama masu kantina da suke kin karbar tsaffin kudi.

A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya yi barazana rufe duk wani banki da ba ya karbar tsohon kudi.

Gwamnan ya soki umurnin hana amfani da tsaffin kudin yana mai cewa zalunci ne tunda babu sabbin kudin isasu a gari.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN