Wasu fusatattun mazauna garin Warri da ke jihar Delta sun lalata shagunan POS. A cewar masu zanga-zangar, ma’aikatan POS na karbar kudade fiye da kima sada hannunsu kafin su basu sabbin takardun naira saboda karancin kudinsa.
Kafin wannan karanci, ma’aikatan POS na karbar Naira 100 kan duk Naira 5000 da aka cire amma da karancin kudin Naira a halin yanzu, suna karbar Naira 1500 kan duk N5000 da aka cire.
Wasu daga cikin ma’aikatan POS sun yi ikirarin cewa sai sun dawo da kudadensu saboda sun sayi takardar Naira daga hannun wasu ma’aikatan banki da ma’aikatan gidan mai.
Kalli bidiyon daya daga cikin POS da aka lalata
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI