Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta rasa dukkanin kujerun Sanata guda uku a hannun jam’iyyar PDP a jihar Kaduna a zaben majalisar dokokin da aka gudanar a ranar Asabar. Intelregion ya ruwaito.
A cikin kujeru uku – Kaduna ta Arewa, Kaduna ta tsakiya, da Kudancin Kaduna – Kudancin Kaduna ne kawai PDP ta mamaye a baya.
A Kaduna ta Arewa Sanata mai ci, Suleiman Abdu Kwari na APC ya sha kaye a hannun Khalid Ibrahim Mustapha na PDP.
Jami’in zabe Farfesa Saleh Ado ya sanar da cewa Khalid ya samu kuri’u 260,026 yayin da Kwari ya samu kuri’u 190,008.
A Kaduna ta tsakiya dan takarar jam’iyyar PDP Lawal Adamu Usman wanda aka fi sani da (Mr. LA) ya samu nasara da kuri’u sama da 250,000.
A cewar jami’in zaben, Farfesa Haruna Aminu, Usman ya samu kuri’u 225,066 a gaban dan takarar APC Abdullahi Mohammad Sani wanda ya samu kuri’u 182,035.
A Kudancin Kaduna, Sunday Katung na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 138,246 inda ya doke abokin takararsa Ayuba Micheal na jam’iyyar Labour wanda ya samu kuri’u 101,479.
Bulus Audu na jam’iyyar APC ya zo na uku da 77,753 kamar yadda jami’in zabe, Abdullahi Dalhatu ya bayyana.
BY ISYAKU.COM
Rubuta ra ayin ka