Zaben 2023: Fitaccen Malamin addini a Najeriya ya bayyana yan takarar shugaban kasa da za su gadi zabe


Babban limamin cocin Citadel Global Community, Fasto Tunde Bakare, bai yi imani cewa Rabiu kwankwaso da Peter Obi za su kai labari ba a zaben shugaban kasa da ke tafe. Legit.ng ya wallafa.

Yayin wani hira a baya-bayan nan, Bakare ya ce idan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (Kwankwaso) da na Jam'iyyar Labour (Obi) za su ajiye banbancin siyasa su hada kai, da sunyi tasiri sosai sun jijiga manyan yan takarar.

Bakare ya ce idan aka yi la'akari da tasirin da Atiku Abubakar da Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, zai yi wahala, su kai ga cimma nasara da takararsu.

Malamin addinin mai karfin fada a ji ya ce:

"Ka yi tunanin idan da Obi da Kwankwaso sun ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu a gefe, suka kafa wata tawaga wacce za ta iya zama madadin wadannan hamshakan masu hannu da shuni, masu gogayya, wadanda suka dade a can, da sun iya girgiza tsarin fiye da yadda suke. yanzu suna yin a matsayin daidaikun mutane suna gudanar da tseren su.

"Da sun girgiza jam’iyyun gaba biyu da sun hada gidajensu amma a yanzu ban ga irin tasirin da za su yi a zaben ba."

A wani abu da ya yi kama da sako ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progress Congress, APC, Asiwaju Bola Tinubu, Fasto Tunde Bakare, ya ce yan siyasa nagari ba su cewa wasu su amsa tambayoyin da aka musu.

Babban limamin cocin na Citadel Global Community Church (tsohon cocin Latter Rain Assembly) ya furta hakan ne cikin jawabinsa kan batutuwan kasa a ranar Lahadi, 15 ga watan Janairu.

Duk da cewa faston bai ambaci sunan Tinubu ba, ya bada misalai da dama da suka nuna cewa yana nufin dan takarar shugaban kasar na APC ne.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN