Type Here to Get Search Results !

Da duminsa: Mutane 3 sun mutu sakamakon arangamar da magoya bayan APC da PDP suka yi a jihar kudu duba yadda ta faru


Akalla mutane uku ne aka ruwaito sun mutu, yayin da wasu kuma suka samu raunuka daban-daban a lokacin da magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, da na jam’iyyar adawa ta PDP suka fafata rikici a lokacin yakin neman zabe na karshe a yankin Surulere na jihar Legas. Jaridar vanguard ta ruwaito.

Sakamakon haka, bangarorin biyu, sun yi kira ga shugaban kasa Muhamnadu Buhari da hukumomin ‘yan sanda da su fara gudanar da bincike cikin gaggawa kan rikicin da nufin kamawa tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Harin dai ya faru ne a ranar Juma’a a yayin ziyarar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Dr Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor ya kai ziyara a wasu unguwanni 245 da ke jihar Legas.

PDP ta yi ikirarin cewa wasu da ake zargin ‘yan bangan siyasa ne masu biyayya ga APC sun je wajen Basaraken, Baale na Ojuoluwa a yankin Empire a karamar hukumar Surulere, inda suka yi masa barazanar cewa ba zai tarbi tawagar ba a ziyarar kwana biyu da ya kai unguwannin Surulere na yankin.

Wadannan na kunshe ne a wata sanarwa ta daban a ranar Juma’a ta bakin kakakin jam’iyyar APC, Seye Oladejo da Hakeem Amode na PDP.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies