Yanzu-Yanzu: An kama wani mai hannu a garkuwa fasinjojin jirgin kasa a Najeriya


Gwamnatin jihar Edo, ranar Lahadi, ta sanar da cewa an kama wani mutum daya da ake zargin yana da hannu a sace Fasinjojin Jirgin kasa a tashar Igueben ranar Asabar. Legit Hausa ta wallafa.

Idan baku manta ba, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa akalla Fasinja 30 yan bindiga suka sace wadanda ke jiran Jirgin kasa a tashar dake karamar hukumar Igueben da misalin karfe 4:00 na yamma.

Da yake jawabi ga manema labarai kan lamarin, kwamishinan sadarwa da wayar da kai na Edo, Chris Osa Nehikhre, ya bayyana harin da abu mai walaha da gwamnati ta taba gamuwa da shi.

Nehikhre ya kara da cewa nan take bayan faruwar lamarin yan sanda da sauran jami'an tsaro suka bazama dazuka da nufin ceto Fasinjojin da kama maharan, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

A cewarsa Kokarin da ake ya fara haifar da sakamako mai kyau domin an kama mutum daya ada ake zargin dan tawagar masu garkuwan ne kuma ya fara bayani.

"Ba tantama jiya ta zo mana da wahala tun bayan shigowar sabuwar shekara, wasu yan bindiga sun sace Fasinjoji 32 a tashar jirgin kasa ta Igueben. Mataimakin gwamna, Philip Shaibu, ya ziyarci wurin."

"Labari mai dadi da ya iso wa gwamnati shi ne daya daga cikin maharan ya shiga hannu kuma ya fara bayanin da zai taimaka wa jami'an tsaro su shawo kan lamarin."

"Gwamnati karkashin gwamna Godwin Obaseki na mika jinjina ga 'yan sanda, 'yan Bijilanti wadanda suka bazama, da ma Mafarautan yankin bisa kokarin da suke na ceto fasinjojin."

Jami'an tsaro sun ceto mutum 5

Daily Trust tace zuwa yanzun rundunar 'yan sanda ta yi nasarar ceto mutane 5 da lamarin ya rutsa da su ciki har da wani jami'in dan sanda da ya yi Ritaya.

Rahoto ya nuna cewa gamayyar jami'an tsaro da suka bazama cikin jejin ne suka samu nasarar kubutar da mutanen cikin koshin lafiya.

Kakakin rundunar yan sandan Edo, Chidi Nwanbuzor, wannan nasara ta samu ne da taimakon sauran hukumomin tsaro hadi da yan Bijilanti da Mafarauta.

Yace:

"Duk da har yanzu bamu tabbatar da yawan fasinjojin da aka sace ba amma mun fara samun nasarori. Daga cikin waÉ—anda jami'ai suka ceto har da dan sanda mai ritaya, wata da jaririnta dan shekara daya da kuma yara mace da namiji."

"Yan sanda da sauran hukumomin tsaro; Dakaraun Edo, yan bijilanti da mafaraunta suna ci gaba da tsefe dajin don ceto Fasinjojin cikin koshin lafiya da kama yan ta'addan."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN