‘Yan sanda sun kashe wasu mutane biyu da ke kai wa ‘yan ta’adda makamai a Zamfara (Hotuna)


Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun kashe wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga makamai a hanyar Gummi zuwa Anka. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 8 ga watan Janairu, 2023, ya ce an kashe masu sayar da makamai ne a wani artabu da ‘yan sanda suka yi.

A cewar PPRO, wadanda ake zargin suna jigilar makaman ne daga jihar Taraba zuwa sansanin ‘yan ta’adda da ke Zamfara a lokacin da ‘yan sanda suka kama su bayan samun bayanan sirri kan motsin su.

Ya kara da cewa wata mota kirar Toyota Corolla dauke da harsashi guda uku na roka RPG, bamabamai guda uku, harsashi mai rai har guda 151 na bindiga kirar AK 47, harsashi guda 200 na bindigar kakkabo jiragen sama (AA) da kuma wasu layukan da aka samu.


Daga ISYAKU.COM

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN