2023: Bayan ganawa da Buhari, shugaban APC ya shure damar Atiku
Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya bayyana cewa za a iya kayar da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa mai zuwa. Legit.ng ta ruwaito. Legit Hausa ya ruwaito.
Adamu ya bayyana haka ne bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari da Aishatu Binani, ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC a Adamawa ranar Juma’a 6 ga watan Janairu.
A ra’ayin Adamu, tasirin Atiku da mulkin PDP a Adamawa ba zai rage wa APC damar samun nasara a jihar Arewa ba.
Daga ISYAKU.COM