Kakakin Rundunar SP Nafi’u Abubakar ya ce an sami hatsarin mota da ya faru a ranar Lahadi da misalin karfe 11:00 na dare inda wata babbar mota ta kwace wa direban a kauyen Malisa da ke kan hanyar Aliero zuwa Sokoto.
Abubakar ya ce motar mai lamba SRP 442 XA tana jigilar fasinjoji da shanu daga karamar hukumar Illela ta jihar Sokoto zuwa Legas.
“Da isa mahadar Malisa direban babbar motar ya kasa shawo kan motar bayan ta kwace masa inda ta fadi, sakamakon haka, fasinjoji 42 sun samu raunuka daban-daban.
“Da samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ahmed Magaji-Kontagora ya garzaya wurin da lamarin ya faru, inda aka kwashe wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Gwandu, domin yi musu magani.
“Wani likita a asibitin ya tabbatar da mutuwar mutane 18, yayin da sauran wadanda abin ya shafa ke karbar magani a halin yanzu.
"Hakazalika, shanu 16 kuma sun mutu sakamakon hatsarin," in ji shi.
Abubakar ya ce Kwamishinan Yan sandan Jihar Kebbi Ahmed Magaji-Kontagora ya kai ziyarar gaggawa wajen, ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma baiwa fasinjojin da suka jikkata cikin gaggawa bayan ya yi takaitaccen jawabi ga jami'an NURTW.
Daga ISYAKU.COM