Jerin sunaye Scholarship: Wamakko ya dauki nauyin matasa 15 marasa galihu don yin karatu a ƙasashen waje

Jerin sunaye Scholarship: Wamakko ya dauki nauyin matasa 15 marasa galihu don yin karatu a ƙasashen waje


Sanata Aliyu Wamakko (APC-Sokoto ta Arewa) ya bayar da tallafin karatu ga wasu matasa marasa galihu su 15 daga jihar don yin karatun digiri a fannin Kimiyya da Injiniya a kasar waje.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Wamakko, Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa kuma tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato a halin yanzu yana daukar nauyin ‘yan asalin jihar sama da 500 da ke karatun kwasa-kwasai daban-daban a ciki da wajen Najeriya.

Wannan ci gaban na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bashar Abubakar, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kai ya raba wa manema labarai a Sokoto ranar Litinin.

A cewar Abubakar, dalibai 15 da suka yi nasara kuma suka cancanta duk an ba su takardar izinin shiga da kuma biza a shirye-shiryen tafiya Jamhuriyar Pakistan nan ba da dadewa ba.

Ya zayyana ‘yan takarar da suka hada da: Abdulkadir Abubakar da Abubakar Sadiq, wadanda za su karanci Masters of Business Administration, yayin da Auwal Aminu da Sagir Abubakar za su karanci Pharmacy da BS Social Sciences, bi da bi.

“Hakazalika, Sa’idu Aminu zai karanci BS Media and Mass Communication, Ahmed Maccido da Naziru Abubakar zasu karanci BS Diet and Nutritional Sciences, yayin da Musa Bello da Mande Kasimu zasu karanci BA Business Administration. 

“Sauran su ne: Saifullahi Shehu, BS Visual Communication Design, Salamatu Umar da Gaddafi Abubakar, wadanda za su yi karatun BS Computer Science, Mukhtar Sadiq da Al’amin Alkali za su karanci BS Electrical Engineering da Yasir Mahe, sun samu BS Social Science,” inji shi.

Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN