Rikici ya barke tsakanin Yan sanda da yan kasuwar Alaba rago a Lagos, an harbe mutum daya

Rikici ya barke tsakanin Yan sanda da yan kasuwar Alaba rago a Lagos, an harbe mutum daya


A ranar Talatar da ta gabata ne mutum daya ya samu raunuka sakamakon harbin bindiga da aka yi tsakanin ‘yan sanda da ‘yan kasuwa a kasuwar Alaba Rago da ke unguwar Ojo a jihar Legas.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya tattaro cewa rikicin ya fara ne bayan da jami’an ‘yan sanda daga sashin Okokomaiko suka mamaye kasuwar domin kama wani da ake zargi.

An tattaro cewa wasu ‘yan kasuwa sun jawo wa jami’an cikas wajen gudanar da ayyukansu.

Daga karshe dai turjiya ta haifar da rikici inda mutum daya ya samu rauni.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, ‘yan sandan da suka je kasuwar domin cafke wani da ake zargi sun harbe shi ne a kokarin ja da baya daga harin.

“’Yan sanda reshen Okokomaiko a yau sun shiga kasuwar Alaba Rago domin aiwatar da kama wani da ake zargi amma sun fuskanci babban hari daga ’yan kasuwa da dama.

“A wani yunkuri na ja da baya da dabara daga harin da ‘yan kasuwar suka kai, daya daga cikin jami’an ya harba makamin da ya yi sanadiyar raunata daya daga cikin maharan.

"An fara cikakken bincike kan musabbabin faruwar lamarin nan take," in ji shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN