Wasu ma'aikatan fadar Shehun Borno 3 sun kone kurmus a hadarin mota, duba yadda ta faru


Wasu ma’aikatan fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Ibn Garbai El-kenmi, sun mutu a wani hadarin mota da ya rutsa da su a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu
.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a Borno, Utten Iki Boyi, ya tabbatar wa Daily trust faruwar lamarin a ranar Talata 24 ga watan Janairu.

Boyi ya ce mutane shida ne suka yi hatsarin wanda ya afku a ranar Litinin, 23 ga watan Janairu, amma an ceto uku kuma an garzaya da su asibiti.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a kusa da yankin Benisheik a lokacin da motar ta abka da wuta.

“Nan da nan muka samu rahoton, tawagarmu ta garzaya wurin da lamarin ya faru, mutane uku sun kone kurmus, an ceto uku kuma an kai su babban asibitin Benishiek domin yi musu magani. Ina tabbatar muku da cewa, abin takaici, mutane uku sun rasa rayukansu.”  Yace.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN