"Ina so in zama Uwargidan Shugaban kasa ta Yarbawa ta farko," matar Atiku ta roki jama'a a wata sabuwar hira
Uwargidan Atiku Abubakar, Titi ta yi kira ga ‘yan kabilar Yarbawa da su tabbatar sun zabi mijinta da ke neman kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP. Legit.ng ya wallafa.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Titi yayin da take magana yayin wata tattaunawa a ranar Talata, 24 ga watan Janairu, ta ce Yarbawa ba su yi alfahari da uwargidan shugaban kasa ba tun lokacin da aka fara mulkin dimokradiyya a 1999.
Da take kira ga al’ummar yankin kudu maso yamma da su marawa mijinta baya, Titi ta ce tana son zama uwargidan shugaban kasar Yarbawa ta farko a Najeriya.
A yayin hirar da BBC Yarabawa ta yi, Titi ta tabbatar wa da jama'a cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyukan jin kai da ya shafi mata da suka hada da yaki da fataucin yara da ayyukan yi.
Har ila yau, ta bayyana cewa mijin nata zai hada kan al’ummar Najeriya idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, Titi ta ce Atiku yana so ya taimaka wa al’umma.