Tarihin kuskure har da asarar da talakawa suka tafka wajen dora shugabanci a takaice

Tarihin kuskure har da asarar da talakawa suka tafka wajen dora shugabanci a takaice


Tarihi ya nuna cewa dole al'umma su fuskanci matsala matukar sun bi son zuciya wajen dora shugabannin bisa raayinsu koma-bayan cancanta. 

Tarihi ya nuna cewa lamari ya maimaita kansa shekaru aru-aru da yawa, inda masana da wadanda suka shaida lamarin suka tabbatar cewa an yi wani shugaba da ya labe da gaskiya don yaudarar jama'a a yarda da shi.

Daga bisani bayan talakawa da matalauta suka amice da shi sai ya saka masu ta hanyar dandana masu ukuba.

An samo cewa wannan shugaban na adawa da kwanciyar hankalin talakawa kuma masana sun yi itifaki cewa HARAMUN ne talaka ya samu kwanciyar hankali ko arziki a zamaninsa.

Tarihi ya tabbatar cewa babban kuskure da dora wanda aka tsine wa Albarka kan karagar shugabanci shi ne janyo wa talaka kunci da matsin rayuwa ba tare da jin tausayi ba don tun asali mahaluki ne mai fama da la'antar dibar Albarka kamar yadda wata majiya ta ambato. 

Daga shafin ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN