An bayar da rahoton cewa, wani mutum mai shekaru 71 da haihuwa ya fadi ya mutu a lokacin da suke shakayawa da wata mata ‘yar shekara 22 a wani masauki a wuraren shakatawa da ke birnin Nairobi na kasar Kenya. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Mutumin da ya shiga dakin da budurwar da karfe hudu na yamma, ya fara haki bayan sa'o'i biyu sannan kuma ya koka da ciwon kirji da baya.
Cikin dakika kadan, hannayensa da kafafunsa sun daina aiki, lamarin da ya sa matar ta nemi taimako daga wani direban tasi da ke tsaye a kofar ginin.
An garzaya da shi asibitin Aga Khan inda aka tabbatar da mutuwarsa da isarsa. An kai gawar marigayin zuwa dakin ajiyar gawa da ke kusa da inda ake ci gaba da gudanar da bincike.
Daga isyaku.com
Rubuta ra ayin ka