Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta tsawaita wa’adin daina karbar katin zabe na dindindin zuwa ranar 5 ga watan Fabrairun 2023, Channels Tv ta rahoto.
INEC ta tsayar da ranar 31 ga watan Janairu matsayin ranar da za a daina karbar katin zaben dindindin amma kwamishinan hukumar, Festus Okoye yace an tsawaita tare da kara wa’adin don baiwa ‘yan Najeriya damar karbar katikansu.
Karin bayani na tafe…
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI