Karfin hali: Har CID hedikwata wani mutum ya kai wa yan sanda cin hancin N1m don a sako mai garkuwa da mutane, duba abin da ya faru

Karfin hali: Har CID hedikwata wani mutum ya kai wa yan sanda cin hancin N1m don a sako  mai garkuwa da mutane, duba abin da ya faru 


Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano, ta ce ta kama wani Bamuwa Umaru, mai shekaru 62, da laifin bayar da cin hancin Naira miliyan 1 domin a sako wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne.

Kakakin rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Haruna-Kiyawa ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano ranar Talata.

“A ranar 16 ga Disamba, 2022 da misalin karfe 2:00 na rana, Bamuwa Umaru, mazaunin garin Shika jihar Kaduna, ya tunkari jami’in da ke kula da masu yaki da masu garkuwa da mutane, sashin binciken manyan laifuka na jihar Kano, SP Aliyu Mohammed.

“Wanda ake zargin ya bayar da Naira miliyan 1 a matsayin cin hanci domin a sako wani da ake zargin mai garkuwa da mutane, Yusuf Ibrahim, mai shekaru 27 a kauyen Danjibga, jihar Zamfara,” inji shi.

Haruna-Kiyawa ya ce, tawagar ‘Operation Restore Peace’ karkashin jagorancin CSP Usman Abdullahi, DPO Rijiyar Zaki Division Kano ne suka kama wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne.

“Wani direban da suka yi garkuwa da shi a hanyar Funtuwa-Gusau ne ya gano Yusuf Ibrahim, kuma suka karbi kudi naira 500,000 a matsayin kudin fansa kafin a sako shi.

“A binciken farko, Ibrahim ya amsa laifinsa sannan ya kara da cewa ya shiga cikin jerin garkuwa da mutane a kauyukan Sheme, Yankara, Faskari da Kucheri dake jihar Katsina da Zamfara.

“Ibrahim ya kuma yi ikirarin cewa kungiyarsu ta kashe kusan 10 daga cikin wadanda aka sace, kuma shi kadai ya kashe biyu daga cikin wadanda aka sace.

"Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike," in ji shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN