Rikici ya barke, matasa sun kashe Hakimi, an sanya dokar hana fita a garin Lambata jihar Neja
An kashe hakimin kauyen Lambata da ke karamar hukumar Gurara a jihar Neja Mohammed Abdulsafur a wani rikici da ya barke tsakanin matasa da yammacin ranar Asabar, 14 ga watan Janairu. Shafin isyaku.com ya samo.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Abdulsafur ya rasu ne sakamakon raunukan da wasu matasa suka yi masa da suka kai masa hari.
Gwamnatin jihar Neja ta sanya dokar hana fita a garin Lambata daga ranar Lahadi zuwa wani lokaci, saboda lamarin.
Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Ahmed Ibrahim Matane, ya ce dokar hana fita za ta kasance daga karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.
Matane ya ce dokar hana fita za ta taimaka wa jami’an tsaro wajen daidaita al’amura a yankin, da ceton rayuka da tabbatar da dawo da doka da oda.
Ya kara da cewa;
"Gwamnati ta yi Allah wadai da tashe-tashen hankula da rashin bin doka da oda da aka yi a garin Lambata"
Marigayi hakimin kauyen, wanda ya yi ritaya a matsayin jami’in kula da shirin cutar kuturta da tarin fuka, ya bar mata daya da ‘ya’ya 13.
Daga ISYAKU.COM