Ko sanyi na da alaka da yawaitar tashin aljanu da iskokai? - Cikakken rahotu

Ko sanyi na da alaka da yawaitar tashin aljanu da iskokai?


Lokacin sanyi, kamar kowane yanayi yakan zo da irin nasa abubuwan.

Kuma duk da an fi alakanta yawaitar cututtuka da yanayin zafi, ita kuma matsalar kwakwalwa musamman tabin hankali da tashin aljanu ko iskokai, an fi alkanta su da yanayin sanyi.

Ko a cikin barkwanci, akan alakanta wanda ya yi wani shirme ko ya yi wani abu da hankali ba zai dauka ba, da cewa ai sanyi ne.

Irin wannan ne abin da ya faru da wata mai suna Maryam Haruna a lokacin wani sanyi shekara hudu da suka gabata.

Maryam Haruna ta shaida wa Aminiya cewa a matsayinta na babbar kawa ga wata da za ta yi aure, ta je gidansu kawar tata domin zuwa kasuwa su yi sayayya.

Ta ce ita da kawar tata sun fita, salin alin suna tafiya suna tattaunawa yadda bikin zai kasance.

Sai dai da shigar su kasuwar ke da wuya, Maryam ta fara jin wani irin yanayi da ba ta saba ba.

“Ni dai kawai farkawa na yi na ga mutane a kaina a gida an yi tagumi ana kallona, sannan na ji duk jikina ya mutu.

“Nan ne aka fada min cewa da muka shiga kasuwar na fara iface-iface ina birgima.

“Amaryar da muka je ce da taimakon wasu suka kai ni wani shago aka kwantar har barci ya dauke ni, aka sa ni a Daidaita Sahu aka kawo ni gida.

“Tun daga nan na fara zuwa ana yi min rukiyya,” inji Maryam.

Maryam ta kara da cewa, “Ni kaina ba sai an fada min ba, na fi shan wahala lokacin sanyi, domin wani lokacin sai in kwana hudu ban san inda kaina yake ba.

“Baya ga fama da ciwon kafa da baya da uwa uba ciwon kai. Ko fita ba na iya yi saboda za a iya make ni in fadi a ko’ina.

“Matsalar aljanu ba ta da dadi, shi ya sa nake jin bacin rai a ce wai matasa na shan kwaya don su fice daga hayyacinsu, ni da da yadda zan yi na sakan daya kada in fita hayyacina in yi abin da ban sani ba so nake.

“Kin ga fa ko a Islamiyya ba kowace surar Kur’ani za a karanta da ni ba a buge ni ba.

“Ga fama da bacin rai ba abin da aka kai min. Ko aljanin ya zo, ya yi ta yi wa malamaina rashin kunya ban ji ban gani ba dole ni zan dauki laifin.

“Amma bayan mahaifina ya je da kansa ya fada a duk makarantar da na shiga sai su yi min karatu da sun ga haka,” in ji ta.

Ta ce, “Sannan ba na iya zuwa bakunta wani waje in kwana ko in wuni, sai da wanda zai kula da ni, musamman da sanyi.

“Idan ya zo daina jin kida ko kallon finafinai nake yi saboda yanzun nan za su zo ina fara kallon.”

Wata mai suna Shahida Dahiru mai larurar tsoron shiga mutane (Socio-phobia) da tsananin damuwa (Depression) ta ce lokacin sanyi ta fi shiga tashin hankali da fargaba.

“Da farko rukiyya babanmu ya rika kai ni saboda daga lokacin da na kai shekara 14, na fara yawan shiru da kebe kaina da gudun mutane, har da kokekoke ko a makaranta.

“Ba na mantawa shugaban makarantarmu ne ya ba shi shawarar ya kai ni wurin likitan kwakwalwa a Dawanau, tunda ko an min rukiyya ba aljanu.

“Da kyar babana ya yarda saboda abokansa na fada masa mahaukata ne kadai ke zuwa can.

“Daga karshe mamata ta yi nasarar shawo kansa ya kai ni, aka ba ni magunguna da shawarwari, shi ke nan na samu sauki.

“Da ko barci ba na iya yi, ga koke-koke, kuma idan an shiga mutane ba ni da natsuwa da na dawo gida sai in firgice in gigice.

“Amma fa duk da haka da sanyi ina jin jiki,” in ji Shahida.

Aminiya ta tuntubi masana kiwon lafiya don rarrabe tsakanin tsakuwa da tsaba.

Shugaban Cibiyar Magungunan Musulunci ta Aba Zarril Gifari, Dokta Isa Lawan wanda aka fi sani da Mai Fada da Aljana, ya ce dalilin da ya sa aka fi samun tashin aljanu ko kamuwa da larurar a lokacin sanyi shi ne karfin kadawar iska.

“Iska ta fi kadawa a lokacin sanyi, kuma shi aljani kansa ma iska ne, don abin da ya sa Bahaushe yake kiran larurar da iska ko tashin iskokai ke nan.

“Idan misali a wani lokacin da ba na sanyi ba aljani zai kwashi minti uku daga bangon duniya zuwa Kano bai isa ba, a lokacin sanyi minti daya ko kasa da haka ya ishe shi, saboda iska ta fi sauri da kadawa.

“Sannan kamar yadda aka sani aljanu sun fi sha’aninsu da daddare, kuma lokacin sanyi dare ya fi rana tsawo.

“Shi ya sa Annabi (SAW) ya hore mu da dagewa da ibada a wannan lokaci. Kin ga riba biyu ke nan, ga ibadar kara samun kusanci da Allah, ga kuma kariya daga aljanu,” in ji shi.

Mahangar likitoci:

Dokta Auwalu Abubakar likitan kwakwalwa ne a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, ya ce a likitance duk da babu larurar da ake kira da aljani ko iskokai, amma akwai larurorin tunani da kwakwalwa da suka fi tashi a lokacin sanyi.

“Mu a likitance ba mu san wata larura ta aljanu ko iskoki ba.

“Abin da muka sani shi ne wani dalili ya hana wasu sassan jiki, ko sinadaran jiki su yi aiki yadda ya kamata, ko kuma karancinsu ya sa kwakwalwa ko zuciya ko wani bangare da ya shafe su yin aiki ba yadda ake so ba.

“Don haka akwai larurori irin su hawan jini, ko wadanda suka shafi zuciya ko kwakwalwa da tunani irin su damuwa da aka fi samun tashinsu a wannan lokaci,” in ji shi.

Ya ce, “Abubuwa da yawa na ba da gudunmawa wajen faruwar haka, daga ciki akwai takaitar ziga-zirgar mutane saboda hazo da sanyin kansa, tunda sanyi na hana mutane fita. Wannan na sa masu larurar hawan jini ko damuwa su samu motsawar ciwon.

“Sannan rashin hasken rana kamar lokacin da ba na sanyi ba, kan sa wasu sinadarai da jiki ke bukata su yi karanci, ko ya zama babu su, wanda shi ma yana ba da gudunmawa wajen motsawar wasu larurorin,” in ji shi.

Ina mafita?

Malam Lawan cewa ya yi mafita daya ce ga masu larurar aljanu ko iskokai a lokacin sanyi, wato amfani da abin da Annabin Allah (S.A.W) ya ce.

“Mai gudun kamuwa da cutar, ya dage da ibada da yawan sauraron karatun Alkur’ani, saboda shi Alkur’ani waraka ne kamar yadda Annabi ya fada,” in ji Malam Lawan.

Shi kuwa Dokta Auwalu Abubakar cewa ya yi, dagewa da shan magani da ganin likita a-kai-a-kai shi ne zai rage kaifin larurorin kwakwalwa.

“A wannan lokacin kamar yadda muke shawartar mutane, musamman masu larurar hawan jini da damuwa, shi ne su rika kokarin hana kansu kebewa suna tunane-tunane, sannan su rika yawan zuwa ganin likita da sun ji alamun ciwonsu zai motsa.

“Akwai abubuwa da dama da za su yi amma wadannan su ne na riga-kafi da kuma agajin gaggawa,” in ji Dokta Abubakar.

Rahotun Jaridar Aminiya

Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN