Kotu ta kori dan takarar PDP daga shiga zaben 2023


Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta soke tikitin dan takarar jam'iyyar PDP na mazabar mamban majalisar wakilai mai wakiltar Abor Mbaise/Ngor Okpala, jihar Imo, Albert Agulanna. Legit.ng ya ruwaito
.

Yayin yanke hukunci kan ƙarar da Uzoma Ugochukwu ya shigar gabanta, Kotun a ranar Jumu'a ta umarci jam'iyyar PDP ta sake sabon zaben fidda gwani a mazabar cikin kwanaki 14.

Jaridar Punch ta tattaro cewa Mazaɓar Aboh Mbaise/Ngor Okpala nan ne mazaɓar tsohon gwamnan jihar Imo wanda ya gabata watau Emeka Ihedioha.

Wannan ci gaban na zuwa ne kasa da mako ɗaya bayan Kotun koli ta soke tikin dan takarar Sanatan Imo ta yamma a inuwar PDP, Jones Onyereri, a cewar rahoton The Nation.

Ana zargin tsohon gwamna Ihedioha da kulla makircin da ya haddasa korar dan takarar Sanata, Mista Onyereri, haka kuma ana ganin Sakataren PDP na kasa, Samuel Anyanwu, ne ya jawo Kotu ta kori Agulanna.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Ihedioha da Anyanwu sun numa sha'awar tikitin takarar gwamnan jihar Imo a inuwar jam'iyyar PDP.

Haka nan alamu sun nuna da yawan mambobin jam'iyyar PDP a jihar sun shiga damuwa kan rigingimun da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa a cikin jam'iyya.

Amma mai magana da yawun PDP a jihar Imo, Collins Opuruozor, ya ce:

"Maƙiyan jam'iyyar PDP wadan da gabansu ya fadi sakamakon ganin yadda mutane suka amince da ita ne suke amfani da Kotu domin fidda PDP daga shiga zaɓe."

Gwamnan jihar Ribas kuma jagoran gwamnonin G-5, Nyeson Wike, ya gargadi kwanitin kamfen Atiku ya nesanta kansa da filin wasan Adokiye Amiesimaka.

A cewar gwamnam duk da gwamnatinsa ta amince Atiku ya yi kamfe a wurin, ba zata yarda wani ya fara nuna iko da filin ba wata ɗaya kafin ranar taron.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN