Buhari bai amince da karin farashin man fetur ba" Minista ya tona asirin yadda ta faru, ya ba yan Najeriya hakuri

"Buhari bai amince da karin farashin man fetur ba" Minista ya tona asirin yadda ta faru, ya ba yan Najeriya hakuri


Abuja, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta amince da wani karin farashin Premium Motor Spirit (PMS) da aka fi sani da man fetur ba. Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

A cikin wata sanarwa, a ranar Juma’a a Abuja, Sylva ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai amince da karin farashin famfon na PMS ba kamar yadda ake yawatawa da labarin.

“Shugaba Muhammadu Buhari bai amince da karin farashin PMS ko man fetur ba a kan haka.

“Babu wani dalilin da zai sa Shugaban kasa ya karya alkawarin da ya yi a baya na cewa ba zai amince da karin farashin PMS a wannan lokaci ba. 

“Shugaban kasa ya damu da halin da talakan Najeriya ke ciki, kuma ya sha fadin cewa ya fahimci kalubalen talakan Najeriya kuma ba zai so ya jawo wa masu zabe wahala ba.

"Gwamnati ba za ta amince da duk wani karuwar farashin man fetur ba a asirce ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba," in ji shi.

Ya ce Shugaban kasar bai umurci Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) ko wata hukuma da ta kara farashin man fetur ba.

A cewarsa, wannan ba lokaci ba ne na duk wani karin farashin mai ba.

“Ina kira ga ’yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda yayin da gwamnati ke aiki tukuru don ganin an samar da man fetur da rarrabawa a kasar yadda ya kamata,” inji shi.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN