An kori basarake daga mukaminsa bayan an tube masa rawanin sarauta sakamakon alaka da yan bindigan a Katsina

An kori basarake daga mukaminsa bayan an tube masa rawanin sarauta sakamakon alaka da yan bindigan a Katsina


Majalisar Masarautar Katsina ta sanar da korar Hakimin Bakori, Makaman Katsina, Idris Sule Idris, bisa zarginsa da taimakawa ta’addanci a yankinsa.

A wata wasika da jaridar Premium Times ta fassara kuma mai kwanan wata 19 ga watan Junairu, 2023, Kauran Katsina, wanda shi ne Hakimin Rimi, Aminu Nuhu Abdulkadir, ya ce an kori Makaman ne bayan da kwamitin gwamnatin jihar ya same shi da laifin tuhume-tuhume da mutanensa ke yi masa.

“Bayan wata wasika da majalisar Masarautar ta samu daga ofishin sakataren gwamnatin jiha mai lamba SEC/54/Vol. VI/1416, inda gwamnan zartaswa ya tabbatar da cewa zarge-zargen da ake yi masa gaskiya ne, batutuwan da aka kawo game da kai.  sun kawo tabarbarewar zaman lafiya a yankinku, don haka majalisar masarautar na son sanar da kai cewa an sauke ka daga mukamin ka na Makaman Katsina Hakimin Bakori,” Mista Abdulkadir, wanda shi ne babban Sarki a masarautar.

Mai magana da yawun Masarautar, Ibrahim Bindawa, ya tabbatar wa Premium Times sallamar.


Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN