Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wani mutum mai suna Issa Naigheti bisa zarginsa da yin garkuwa da mahaifinsa tare da karbar kudin fansa N2.5m.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Ajayi Okasanmi, ya ce jami’an rundunar da ke yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ne suka kama wanda ake zargin a unguwar Kambi da ke Ilorin.
An ruwaito Naigheti ya amsa laifinsa. Okasanmi ya ce;
“Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da hada baki da wasu mutane biyu domin yin garkuwa da mahaifinsa, Bature Naigboho a yankin Igboho/Igbeti a jihar Oyo tare da karban kudin fansa N2.5m.”
Okasanmi ya kuma kara da cewa za a mayar da shari’ar zuwa jihar Oyo, inda nan ne aka aikata laifin.