Da duminsa: ‘Yan sanda sun dakile yunkurin yin garkuwa da Kakakin Majalisar wata Jihar arewa


Jos – Rundunar ‘yan sandan jihar Filato a daren Juma’ar da ta gabata 6/1/2023 ta dakile yunkurin wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sace kakakin majalisar dokokin jihar Yakubu Sanda. Jaridar vanguard ta ruwaito.

An ce da misalin karfe 11 na dare ne wasu ‘yan bindiga suka bi sawun shugaban majalisar a cikin wata mota kirar Honda CR-V mai launin toka zuwa gidansa da ke karamar hukumar Jos, amma mutanen uku da ke cikin motar suka yi yunkurin kai hari.  Sun yi yunkurin shiga gidansa don su kama shi. Sai dai jami’an ‘yan sanda da ke aikin gadi a gidan suka fuskance su, sannan kuma jami’in ‘yan sanda na Dibisional (DPO) reshen Rantya, SP Ayuba Iliya da jami’an sa suka kawo dauki nan take suka bayar agaji ga Yan sandan da ke aikin gadi a gidan suka fatattakar maharan.

DSP Alfred Alabo, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, “Yaki da muggan laifuka da aikata laifuka Yan sanda za su ci gaba da fuskantarsu  a jihar".

Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN