Jaruma Elsie Okpocha, tsohuwar matar mai wasan barkwanci Basketmouth, ta bukaci mata su kaurace wa aure da ke iya ba mata kunya. Shafin isyaku.com ya samo.
A wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram, mahaifiyar yara uku ta ce:
"Yana da kyau ku fahimci cewa idan mace bata yi aure ba, watakila tana taka tsan-tsan ne ko kuma bata sami wanda ya dace da ita bane, ba wai a gaggauta yin aure ba, domin aure na tattare da kalubale. Idan mace ta ce bata shirya ba, kada ku kalubalance ta da kalamai na cutarwa".
Idan baku manta ba, a watan Disamba 2022 Basketmouth ya sanar cewa aurensa da matarsa na tsawon shekara 12 ya zo karshe.
Kalli bidiyo a kasa: