Kotun Daukaka Kara ta soke Hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta haramta wa Jam’iyyar PDP shiga zaben Gwamnan Jihar Zamfara a 2023. Jaridar Aminiya ta ruwaito.
Kotun Daukakarar da ke zamanta a Sakkwato ta tabbatar Dauda Lawal Dare a matsayin halastaccen dan takarar PDP a zaben da ke tafe a watan Maris.
Hakan kuwa na zuwa ne bayan da farko Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara ta soke zaben da Dauda Lawal ya lashe a matsayin dan takarar gwamnan PDP na Jihar Zamfara.