An kama barawon mota da ya addabi jama'a da satar motoci a jihar arewa


Rundunar Yan sandan jihar Bauchi ta kama wani kasurgumin barawon mota dan shekara 32 mai suna Muhammed Bashir bayan ya sace mota kirar Toyota Corolla
. Shafin isyaku.com ya samo.

Kakakin rundunar Yan sandan jihar SP Ahmed Mohammed Wakil ya sanar da haka ranar Alhamis 5 ga watan Janairu.

Ya ce wanda a aka kama ya zo ne daga Kano tare da abokansa da suka tsere a halin yanzu, domin su yi satar mota a Bauchi.

Ya ce Bashir ya sace motar ne a garejin wani bakanike a kan hanyar Saidu Zungur da ke Bauchi.


Yan sanda sun Sami takardar shaidar NSCDC tare da makullan mota guda uku a wajen Bashir.

Ya shaida wa Yan sanda cewa shi jami'in taimako ne volunteer a rundunar NSCDC kafin a kore shi. 

Wakil ya ce an damke Bashir ne yayin da yake kokarin guduwa da motar sakamakon sintirin gaggawa da Yan sanda suka yi bayan samun rahotun satar motar.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN