Kebbi: Mutum 18 sun mutu, 42 sun sami raunuka, shanu 16 sun mutu a mumunar hatsarin mota da ya afku


Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane 18 a lokacin da wata babbar mota da ke jigilar fasinjoji da shanu ta yi hatsari a kauyen Malisa da ke karamar hukumar Gwandu a jihar. Kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito.

Kakakin Rundunar SP Nafi’u Abubakar ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Litinin.

Ya ce hatsarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 11:00 na dare inda motar ta kwace wa direban a kauyen Malisa da ke kan hanyar Aliero zuwa Sokoto.

Abubakar ya ce motar mai lamba SRP 442 XA tana jigilar fasinjoji da shanu daga karamar hukumar Illela ta jihar Sokoto zuwa Legas.

“Da isa mahadar Malisa direban babbar motar ya kasa shawo kan motar  bayan ta kwace masa inda ta fadi, sakamakon haka, fasinjoji 42 sun samu raunuka daban-daban.

“Da samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ahmed Magaji-Kontagora ya garzaya wurin da lamarin ya faru, inda aka kwashe wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Gwandu, domin yi musu magani.

“Wani likita a asibitin ya tabbatar da mutuwar mutane 18, yayin da sauran wadanda abin ya shafa ke karbar magani a halin yanzu. 

"Hakazalika, shanu 16 kuma sun mutu sakamakon hatsarin," in ji shi.

Abubakar ya ce Magaji-Kontagora ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma baiwa fasinjojin da suka jikkata cikin gaggawa.

“CP ya yi kira ga NURTW, NARTO da sauran masu amfani da hanyar da su tabbatar da cewa sun samar da isassun matakan tsaro a cikin motocinsu kuma su kasance masu hankali yayin tuki, da nufin hana afkuwar lamarin nan gaba.

Ya kara da cewa "Ya kamata su kiyaye iyakar saurin gudu, su guji yin lodi fiye da kima, rashin hankali da kuma taka tsantsan yayin tuki," in ji shi

Daga ISYAKU.COM

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN