Duba jihohi 2 da APC za ta iya kwacewa daga PDP a zaben 2023, ga dali...

Duba jihohi 2 da APC za ta iya kwacewa daga PDP a zaben 2023, ga dali...


Jam'iyyun siyasa na ta yin martani da kokarin ganin nasara ya zo bangarensu yayin da ake ci gaba da yakin neman zaben 2023 cike da dabaru. Sai dai kuma, jam'iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) na ta shirya dabarun cin galaba kan juna kasancewarsu jam'iyya mai mulki da babbar mai adawa a kasar. Kamar yadda legit.ng ya wallafa.

Jihohin PDP da APC ke zawarci a zaben 2023

 Shakka babu jam'iyyar APC na yunkurin ganin ta kwato wasu manyan jihohi biyu da PDP ke jan ragamarsu a babban zabe mai zuwa. 

A ranar Asabar, 14 ga watan Janairu, Bashir Ahmad, mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ta musamman a kafofin sadarwar zamani, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa shugaban kasar zai yi kamfen din shugaban kasa na APC a jihohi takwas.

Manyan jihohi biyu da ke cikin jerin suna karkashin ikon PDP ne. 

Sune:

Bauchi 

Akwa Ibom 

Jihohin biyu sun kasance masu karfin tattalin arziki domin dai suna samar da man fetur. Koda dai Bauchi jihar arewa ce yayin da Akwa Ibom ta kasance a kudu maso kudu, jihar ta arewa na daya daga cikin jihohin arewa biyu da aka fara hakar mai a kwanan nan, karfin tattalin arzikinta zai zama mai matukar amfani ga jam'iyyar APC mai mulki.

An shirya dabaru a yakin neman zaben shugaban kasa na APC a 2023 domin dai shugaban kasar ya hallara ne kawai a gangamin yakin neman zaben jam'iyyar na Jos da Adamawa.

Gangamin na Jos da shine aka bude kamfen din yayin da watakila shugaban kasar ya hallara a Adamawa ne saboda jam'iyyar ta gabatar da yan takara mace, Aishatu Binani.

Binani na takara don tsige Ahmadu Fintiri, dan takarar PDP mai ci wanda ke neman zarcewa a karo na biyu kuma jihar ita ce mahaifar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP. Kalli wallafar Bashir:

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN