Yanzu yanzu: Ta faru, Gwamnan Arewa mai tasiri ya janye daga goyon bayan zaben Tinubu 2023


Rahoton Nigerian Tribune ya yi hasashen gwamnan jihar Kogi kuma mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC, Yahaya Bello, ya janye goyon bayansa ga Bola Tinubu. Legit.ng ya wallafa.

An nakalto wata majiya a rahoton tana bayyana cewa sabon matsayin gwamnan ya biyo bayan lissafinsa a siyasar jihar ta arewa maso tsakiya gabannin zaben gwamnan Nuwamba

Majiyar ta bayyana cewa Gwamna Bello ya shiga halin fargaba kan shugabancin Tinubu.

An tattaro cewa gwamnan na zargin cewa dan majalisa mai wakiltan mazabar Ikeja a majalisar wakilai kuma sakataren kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC na iya shiga tseren neman tikitin gwamnan APC a jihar.

Feleke dan hannun damar Tinubu ne kuma shine abokin tafiyar dan takarar gwamnan APC a zaben Nuwamban 2015, Abubakar Audu, wanda ya rasu jim kadan bayan kada kuri'arsa.

Hadimin Bello ya gargadi gwamnan Kogi da ya janye goyon bayansa ga Tinubu

An tattaro cewa an gargadi gwamna Bello wanda shine jagoran matasa na kwamitin yakin neman zaben Tinubu-Shettima, a kan cewa goyon bayan Tinubu na iya haifar da gwamnatin Faleke a jihar.

Tsoron na kusa da Bello shine cewa Tinubu zai zamo da wuka da nama kan matsayin da kowa zai samu a jam'iyyar idan ya lashe zaben shugaban kasa, inda zai bar ubangidansu a cikin duhu, rahoton Within Nigeria.

Wani jigon jam'iyyar a jihar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce Bello baya goyon bayan mika mulki zuwa yankin Kogi ta yamma inda daga nan ne Faleke ya fito.

An kuma tattaro cewa gwamnan ya rigada ya nuna goyon bayan Akanta Janar a jihar, Jubril Mommoh wanda ya fito daga Kogi ta gabas.

Ya ce:

"Gwamnan na son makusancinsa, wanda zai iya rufe abubuwan da ya aikata a matsayin magajinsa.

"Don haka yana taka-tsantsan da nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa. Ya san cewa Tinubu zai duba yadda ya yi nasara da goyon bayan gwamnonin arewa kuma zai iya la'akari da Kogi ta yamma da Faleke."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN